30 Nuwamba 2015 - 07:33
An kai hari a wani gidan yarin Guinea

Labarai daga kasar Guinea sun ce wasu mutane sun kutsa kai cikin wani gidan kurkuku da karfin tsiya, inda suka kashe bursinoni 4 da ake tsare dasu, wadanda ake zargi da kisan kai.

Wadanda suka shaida faruwar lamarin da kuma wasu jami'ai, sun ce jita-jitar da aka rika yadawa a garin Kouroussa cewa ana shirin sakin mutanen 4, ita ta janyo mutanen garin da suka fusata dannawa gidan yarin.

Ana zargin firsinonin 4 ne da kashe wani dillalin gwal a farkon wannan watan.

Uku daga cikinsu, dukan tsiya ne ya kashe su, yayin da cikon na hudun kuma, kona shi aka yi da ransa.288